Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International a Nijeriya, ta yi Alla-wadai kan cin zarafi da kama wasu ‘yan jarida da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi bisa umurnin kwamishinan yada labarai Ibrahim Waiya, a cewar kungiyar mai kare hakkin dan Adam a kasashen duniya.
Kungiyar na zargin kwamishinan ya ba da umurnin kama Buhari Abba Rano, mawallafin jaridar yanar gizo ta Kano Times da Isma’il Auwal, dan jarida mai zaman kansa, saboda wallafa wani ra’ayi da suka yi.
Amnesty International ta bukaci gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sanda su kare hakkin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin wadannan ‘yan jarida gami da dakatar da yunkurin gurfanar da yan jaridar gaban kotu da zargin yunkurin bata suna.