DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jihohi tara ne kacal daga cikin 36 ke da ingantattun cibiyoyin yaki da miyagun kwayoyi – Buba Marwa

-

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana damuwa matuƙa game da yadda mafi yawan jihohin Najeriya suka kasa kafa ko amfani da kwamitin yaki da miyagun kwayoyi a matakin jihohi.

A cewar Marwa, wannan na daga cikin manyan cikas da ke hana ci gaba wajen yaki da amfani da kwayoyi a faɗin ƙasar nan.

Google search engine

Yayin wani taron horaswa da hukumar NDLEA ta shirya a Abuja ga matan gwamnoni na Najeriya karkashin kungiyar Nigeria Governors’ Spouses Forum, Marwa ya bayyana cewa jihohi tara ne kacal daga cikin 36 da ke da ingantattun kwamitoci masu aiki wajen rage buƙatar amfani da kwayoyi.

Birgediya Marwa ya kuma bayyana bukatar fara gwajin miyagun kwayoyi ga ma’aurata kafin aure, yana mai cewa yawaitar shan kwayoyi na da nasaba da tashin hankali a gidaje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 – Asusun NELFUND

Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan...

Tsohon kwamishinan Ganduje ya soki gwamnatin Abba bisa zargin sayar da filin makarantar

Tsohon kwamishinan ilimi na a zamanin Ganduje, Muhammad Sanusi Sa'id Kiru, ya soki matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da Makarantar Sakandare ta ‘Yan...

Mafi Shahara