Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaMajalisar Dattawa ta amince da sabbin dokokin gyaran haraji -Akpabio

Majalisar Dattawa ta amince da sabbin dokokin gyaran haraji -Akpabio

Majalisar Dattawa ta amince da dokoki biyu daga cikin muhimman dokokin gyaran haraji guda hudu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar a watan Oktoba 2024.

Dokokin da aka amince da su sun hada da:

  • Dokar soke hukumar FIRS (Federal Inland Revenue Service),
  • da kuma dokar kafa sabuwar Hukumar Haraji ta Kasa da asusun hadaka na kudaden Haraji (Joint Revenue Board da Nigeria Revenue Service Bill 2025).

Majalisar ta amince da dokokin ne bayan nazari kai tsaye da karatu na uku a zauren majalisa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce wannan ci gaba zai inganta tafiyar da gwamnati da kuma saukaka tsarin tattarawa da raba haraji a kasar.

Ya kuma ce sauran dokokin biyu za a kammala su a ranar Alhamis, ko da hakan na bukatar tsawaita zaman majalisar.

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata