DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun yi kuskure a sakamakon da muka fitar na dalibai – Hukumar JAMB

-

Cikin alhini da nadamar abin da ya faru, hukumar JAMB da ke shirya jarabawar neman shiga makarantun gaba da sakandare a Nijeriya ta karbi duk wani laifi kan faduwa jarabawar da daliban Nijeriya na bana, 2025 suka yi.

Hukumar ta JAMB ta amince da wasu kurakurai da suka shafi yadda daliban suka fuskanci sakamako mara kyau a jarrabawar ta shekarar 2025, inda ta ce yau da gobe CE ta yi halinta.

Google search engine

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce abin da ya kamata ya kasance lokacin farin ciki ya rikide ya koma wani abu daban saboda wasu kura-kurai daya zuwa biyu, da ya hakan ya nuna dan’adamtaka.

Jarabawar JAMB wani muhimmin ne sharadi ne na samun gurbin karatu a manyan makarantu na gaba da sakandare a Nijeriya. Ana jarraba dalibai ne a fannoni hudu, ciki har da “Amfani da Turanci” wanda ya zama dole, sai sauran uku daga fannin da dalibin ke son karantawa.

Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zauna jarrabawar, fiye da miliyan 1.5 ne suka kasa samun maki 200 daga cikin maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi.

A cewar hukumar, daga cikin sakamako sama da milyan 1,9 da aka tantance, dalibai 4,756 ne kawai wato kaso 0.24% suka samu maki 320 ko fiye, wanda ake dauka a matsayin sakamako na kwarai. Dalibai 7,658 kuma wato kaso 0.39% suka samu maki tsakanin 300 zuwa 319 — jimillar wadanda suka samu maki 300 zuwa sama ya kai 12,414 Ma’ana kaso 0.63%.

Haka nan, dalibai 73,441 wato kashi 3.76% suka samu maki 250 zuwa 299, sannan 334,560 kashi 17.11% suka samu tsakanin 200 da 249.

Dalibai 983,187 wato kashi 50.29% ne suka samu maki tsakanin 160 da 199 — wanda ake ganin shi ne mafi karancin sharadin karba a mafi yawan jami’o’i.

Bugu da kari, 488,197 kashi 24.97% sun samu maki tsakanin 140 da 159; 57,419 wato kashi 2.94% sun samu tsakanin 120 da 139; 3,820 wato kashi 0.20% sun samu tsakanin 100 da 119, yayin da 2,031 kashi 0.10% suka kasa kaiwa maki 100.

Fiye da kashi 75% na daliban da suka zauna jarrabawar (kimanin miliyan 1.5) ba su kai maki 200 ba — maki da ake ɗauka a matsayin matsakaicin sakamako, kasancewar ana jarraba bisa maki 400.

Wasu daga cikin daliban da abin ya shafa sun ce suna shirin kai hukumar JAMB kara kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daga 2026 ₦500,000 kawai ɗan Nijeriya zai iya cira a banki cikin sati ɗaya – CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026. Babban bankin ya...

Ƴan kwangila sun girke akwatin gawa a ofishin ma’aikatar kuɗin Nijeriya

‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.   ‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta 'yan asalin Nijeriya sun...

Mafi Shahara