DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ruwan sama da iska mai karfi ya rusa gidan wasu sabbin ma’aurata a Katsina

-

Akalla gidaje 300 ne suka rushe, tare da asarar dukiyoyi da darajarsu ta haura miliyoyin Naira, sakamakon wani hadari mai karfi tare iska da aka samu tare da ruwan sama a wasu unguwanni a birnin Katsina.

Lamarin da ya dauki kusan mintuna goma sha biyar da yamma bayan sallar La’asar a ranar Laraba, ya haddasa kwarewar rufin gine-gine kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

Google search engine

Daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa akwai Sabuwar Unguwar Modoji, Shinkafi, da yankin Kukar-Gesa, har da Ambassador Quarters da kuma wasu sassan karamar hukumar Jibia.

Mutane da dama, ciki har da wasu sabbin ma’aurata, sun rasa matsugunansu sakamakon wannan iftila’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaban Amurka Donald Trumph ya haramtawa Farfesa Wole Soyinka zuwa kasar

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Donald Trump ta soke takardar izinin shiga ƙasar ga Farfesa Wole Soyinka, sanannen marubuci a duniya. Farfesa Soyinka ya bayyana hakan...

Hukumar agajin gaggawa NEMA ta karɓi ƴan Nijeriya 153 da suka makale a Chadi

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta bayyana cewa ta karɓi ’yan Nijeriya 153 da suka dawo daga ƙasar Chadi, ƙarƙashin shirin Ƙungiyar...

Mafi Shahara