Hukumar ba da agajin gaggawa a Nijeriya NEMA, ta yi kira ga jihohin kasar da su zamo cikin shiri domin tunkarar ambaliyar ruwa da ke iya afkuwa a daminar bana, 2025.
Hukumar ta ce za ta aika tawaga kowace Jiha domin tattataunawa da al’ummar da ake sa ran faruwar ambaliyar domin gargadi da kuma zama cikin shirin ko-ta-kwana.
Darakta Janar ta NEMA, Malama Zubaida Umar ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja.
Sai dai, hukumar ta NEMA ba ta ambaci sunayen jihohi da kananan hukumomin da ake sa ran ambaliyar ruwan za ta afku ba.