Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amsa goron gayyatar da sabon Paparoma Pope Leo XIV ys yi masa zuwa birnin Rome na kasar Italy.
Daga cikin tawagar shugaban kasar hada karamar ministar harkokin kasashen waje Amb. Bianca Odumegu-Ojukwu Arch Bishop Ignatius Kaigama da Mathew Hassan Kukah da sauransu.
Shugaban kasar zai bar Abuja a ranar Asabar ya dawo kasar ranar Talata, 20 ga watan Mayu, 2025.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga mashawarcin Shugaba Tinubu kan harkokin sadarwa ya fitar da DCL Hausa ta samu kwafi.