Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci jami’an rundunonin tsaron Nijeriya da su kara azama wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa zaman lafiyar dimokradiyyar Nijeriya, daidaiton yankin da ci gaban tattalin arziki na da alaka kai tsaye da tsaron kasa, inda ya umurci a dauki matakin karshe kan duk wasu abokan gaba da ke barazana ga zaman lafiyar kasar.
Ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, a yayin bikin karbar sabbin jiragen sama guda biyu samfurin Agusta 109 Trekker, wanda aka shirya a matsayin wani bangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya.
Shugaban, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya jaddada cewa dole ne a karfafa tsaron kasa domin al’ummar Nijeriya su samu damar gudanar da ayyuka masu amfani da kuma habbaka tattalin arzikin kasa.