Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kisan wani na hannun damar Bello a wani hari ta sama ta da kai a yankin karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, rundunar sojin ta ce ta yi nasarar hallaka Alhaji Shaudo Alku ne a Lahadin nan.
Sanarwar ta ce, daga Jamhuriyar Nijar aka gayyato Alhaji Shaudo Alku don zuwa Nijeriya a aikata ta’addanci kafin ya hadu da ajalinsa a hannun sojojin da ke aiki karkashin shirin Operation Fansar Yamma.