Shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Abba El-Mustapha, ya bayar da umurnin soke lasisin wasu gidajen gala takwas a jihar Kano tare da haramta aikinsu cikin gaggawa saboda saba ka’idojin hukumar.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar kuma ya rabawa manema labarai jim kadan bayan kammala taron gudanarwar hukumar.
A cewar sanarwar, gidajen gala 8 da abin ya shafa sun hada da.
1. Hamdala Entertainment (Ungoggo)
2. Lady J. Entertainment (Sanya Olu)
3. Dan Hausa Entertainment (Sanya Olu)
4. Ni’ima Entertainment (Zungeru)
5. Ariya Entertainment (Abedi Sabon Gari)
6. Babbangida Entertainment (Balatus)
7. Harsashi Entertainment (Ebedi Sabon Gari)
8. Wazobiya Entertainment (Sanya Olu)
Abdullahi Sani Sulaiman ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan rashin bin ka’idojin hukumar yasa aka dauki wannan mataki.