Jiga-jigan jam’iyyar APC na yankin Arewa ta Tsakiya da suka hada da gwamnoni da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da sauran masu ruwa da tsaki, sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wani taro da suka gudanar a daren jiya Laraba a Abuja, shugabannin jam’iyyar APC na Arewa ta Tsakiya sun amince da shugaba Tinubu ya zarce a wa’adi na biyu, kamar yadda wata sanarwar da aka fitar ta bayyana.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, Abdullahi Sule na Nasarawa, da Mohammed Umar Bago na Niger, Ahmed Usman Ododo na Kogi, da kuma Hyacinth Iormem Alia na Benue, George Akume. da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje da dai sauransu.
Sanarwar, wacce Gwamna Sule na Nasarawa ya karanta ta ce yankin Arewa ta Tsakiya sun marawa yunkurin Shugaba Tinubu baya na sake tsayawa takara a 2027 don ci gaba da jagorancin Nijeriya.



