Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur a sassa daban daban na Nijeriya, inda a yanzu haka farashin ya koma tsakanin N875 zuwa N905 kowace lita.
Sabon farashin, ya nuna cewa an rage Naira 15 ga kowace lita, kamar yadda aka wallafa a dandalin sada zumunta na matatar Dangote a ranar Alhamis.
Haka farashin yake a hannun manyan dillalan mai tare da haɗin gwiwar matatar, ciki har da MRS, Ardova, Heyden, Optima Energy, Techno Oil, da Hyde Energy.




Ukasha Ibrahim
Ubangiji Allah yakara daukaka, da basira.
Ubangiji Allah yakara kareka daga sherin masu sheri.