Gwamnonin jam’iyyar APC sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara daya tilo na jam’iyyar a zaben 2027.
Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban dandalin gwamnonin APC, Hope Uzodima ne ya bayyana haka a babban taron jam’iyyar da ya gudana a fadar Shugaban Kasa.
Uzodinma ne ya fara ayyana wannan kudiri yayin da gwamnan Kaduna, Uba sani ya mara masa baya inda daga bisani kuma sauran gwamnonin suka amince da Tinubu a matsayin dan takara tilo a jam’iyyar.



