DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Musulmai sama da milyan daya da rabi sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar aikin hajjin bana

-

Hukumomin Saudiyya sun ce ya zuwa yanzu sama da mahajjata miliyan 1.1 ne suka isa kasar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.

Babban daraktan kula da takardun shige da fice ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Google search engine

A cewarsa, jimlar maniyyata 1,102,469 ne suka isa kasar Saudiyya daga kasashe daban-daban ta hanyoyin kan tudu da ruwa da Kuma sararin samaniya a karshen ranar Litinin 26 ga watan Mayu.

Daraktan ya kuma bayyana cewa, daga cikin alkaluman, mahajjata 1,044,341 sun isa ta jirgin sama, inda mutum 53,850 ta kan iyakokin kasa, sauran kuma 4,278 ta tashar jiragen ruwa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara