Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun kawar da wasu ‘yan bindiga guda uku a kauyukan Teng da Kayarda na karamar hukumar Qua’an Pan, a jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa an kai harin ne da safiyar Talata bayan samun sahihan bayanan sirri kan shirin ‘yan bindigar na kai farmaki.
An kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, magazine hudu da harsashi 56 daga hannunsu.
Zhakom ya ce rundunar na ci gaba da neman sauran ‘yan kungiyar da suka tsere kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tabbatar.



