Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa hukumar EFCC da ICPC sun kwato kudade da suka kai Naira biliyan 277 da dala miliyan 105 a cikin shekarar bara ta 2024.
EFCC kadai ta kwato zunzurutun kudi har dala miliyan 245 da wasu dala miliyan 200, yayin da ICPC ta dawo da Naira biliyan 29.685 da kuma dala dubu 966,900 daga hannun baragurbin masu cin hanci da rashawa.
Fagbemi ya bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar a Abuja Continental, inda ya ce an samu nasarar dawo da wasu makudan kudade da aka fitar zuwa kasashen waje.
Wannan Ci gaba a cewar rahoton da gidan talabijin na Channels ya fitar yana kara nuna jajircewar hukumomin yaki da cin hanci a ‘yan kwanakin nan.



