DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar Dattawa ta tabbatar da kasafin Naira tiriliyan 1.8 na FCT na 2025

-

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 1.8 na shekarar 2025 ga Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya (FCTA). Wannan ya biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin FCT a zauren majalisa daga Shugaban Kwamitin, Sanata Bomai Ibrahim daga jihar Yobe ya gabatar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwato cewa, kasafin ya ƙunshi Naira biliyan 106 don albashin ma’aikata, Naira biliyan 352 don kudaden gudanarwa, wanda ya kai jimillar kashe kuɗin yau da kullum Naira biliyan 502.

Google search engine

An kuma ware Naira tiriliyan 1.3 don manyan ayyuka, inda kashi 85% daga ciki zai tafi kan ayyukan da ake gudanarwa, yayin da kashi 50% zai je sabbin ayyuka.

Sanata Bomai ya bayyana cewa an tattauna kasafin ne tare da Ministan Abuja da wasu muhimman jami’an FCTA kafin gabatar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara