Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata doka ta musamman don rage tsadar ayyukan hako mai a bangaren kan tudu wato upstream Kenan.
Takardar daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Makamashi ta ce tsadar aiki na da nasaba da jinkirin kamala ayyuka da ka’idojin local content.
Rahoton Jaridar Daily Nijeriya ya ce dokar ta dogara ne da ikon shugaban kasa a kundin tsarin Mulki da dokar harajin kamfanoni.
Mai ba shugaban kasa, Olu shawara ta musamman Verheijen, ta ce dokar za ta ba da rangwamen harajin ga kamfanonin da suka rage kudin aiki, tare da mayar musu kasha 50% na karin ribar da gwamnati ta samu.



