Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sun caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu saboda amfani da talauci a matsayin makami ga ‘yan Nijeriya.
Jiga-jigan siyasar na jawabi ne a wani da aka gudanar don taya Amaechi murnar cika shekaru 60 a Abuja.
A cewar Atiku, gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami don tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba su juya musu baya ba.
Sh kuwa El-Rufai, yace Najeriya na cikin wani mawuyacin hali da bata taba shiga ba tun 1914.
A gefe daya kuwa, Amaechi yace manufofin gwamnatin Tinubu na cika aljihun wasu mutane kalilan ne a cikin gwamnati.



