Kungiyoyi 104 a Nijeriya ne suka mika bukatar a yi musu rajista don su zama jam’iyyun siyasa ga hukumar zaben INEC.
Kungiyoyin dai sun mika wannan bukata tasu ne bayan zaben shekarar 2023.
Binciken da jaridar Daily Trust ta yi, ya nuna cewa hukumar na ci gaba da jan kafa wajen yi wa jam’iyyun rejista.
Jaridar ta ruwaito cewa daya daga cikin hanyoyin da hadakar ‘yan adawa ke son bi wajen kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, shine fitowa da wata sabuwar jam’iyyar siyasa da za a yi wa rejista mai suna All Democratic Alliance (ADA).
A cewar majiyoyin daga cikin hadakar, wannan shine mafi dacewa saboda akwai zargin cewa jam’iyya mai mulki ta kutsa cikin galibin jam’iyyun adawa da ake da su, kuma za ta iya amfani da su wajen dakile yunkurin kawancen da ake shirin kullawa.



