Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nijeriya ta ce tana binciken wasu mutane biyu da ake zargi da tu’ammali da kudin jabu, inda ta ce an kama su da kudin Dala har $899,800.
Jami’an hukumar NDLEA ne dai suka kama Abubakar Hussaini da Sahabi Adamu a Wudil, kan titin zuwa Maiduguri jihar Borno kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na X.
Sanarwar ta ce mutanen biyu na tafiya ne a cikin wata mota kirar Golf 3 kan hanyar zuwa kauyen Kila da ke karamar hukumar Gwaram a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.



