DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Kano Abba Kabir ya umurci da a binciki musabbabin rage albashin wasu ma’aikatan jihar, har ma ya kafa kwamiti

-

 

Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya kaddamar da kwamitin da zai bincike matsalolin rashin biyan albashi da ya shafi wasu ma’aikatan gwamnati a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis ya bayyana matakin a matsayin cin zarafin ma’aikata da ba za a amince da shi ba da kuma cin amanar al’umma,gwamnan ya sha alwashin fallasa tare da hukunta wadanda suke da hannu wajen aikata hakan.

Ya ce gwamnati ba za ta amince da duk wani zalunci da ake yi wa ma’aikatan ta ba, duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan rashin imani tabbas, zai fuskanci fushin doka.

An umurci kwamitin da ya gudanar da cikakken bincike kan albashin jihar daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance su, tare da ba da shawarar gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Cin hanci la’ana ce, mu tsabtace kanmu daga rashawa- EFCC

A wani sakon tunatarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook albarkacin ranar Juma’a, hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya,...

Babu karar-kwana, da tuni na bakuncin lahira a zanga-zangar #EndSARS – Jarumi a Nollywoood Desmond Elliot

Fitaccen ɗan wasan fina-finan Nollywood kuma ɗan siyasa, Hon. Desmond Elliot, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga wani hari da wasu baƙin fuska suka yi...

Mafi Shahara