Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan, za ta bayyana a kotu ranar Talata, kamar yadda aka bukata.
Jagoran lauyoyinta West Idahosa SAN, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Sai dai Idahosa ya bayyana rashin tabbas ko Gwamnatin Tarayya na da niyyar gurfanar da ita a ranar Talatar.
Ya ce duk da me Gwamnatin Tarayya ke shiryawa, Akpoti-Uduaghan, a matsayinta na mace mai bin doka, za ta yi biyayya ga umarnin kotu.



