Rundunar ‘yan sanda a Kaduna ta kama mutane 13 dauke da makamai masu hadari, bayan kisan wani babban jami’in sojan ruwa, Lt. Commodore M. Buba, a unguwar Kawo.
Lamarin ya faru da safiyar Lahadi, yayin da mamacin ke kokarin canza tayar motarsa da ta fashe. Wani da ake zargin mai satar waya ne ya bukaci wayarsa, amma bayan ya ki bayarwa, sai ya caka masa wuka.
Daga bisani, jama’ar da ke wurin suka farmaki barawon har sai da ya rasa ransa. An garzaya da sojan zuwa asibitin Manaal, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa. Rundunar ta ce ana cigaba da bincike.