DCL Hausa Radio
Kaitsaye

MKO Abiola ne ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni – IBB

-

 

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce marigayi Basorun Moshood Kashimawo Olawale Abiola ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

IBB ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “A Journey in Service” wanda aka kaddamar a Abuja ranar Alhamis.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo wanda ya duba littafin ya ruwaito Babangida na cewa Marigayi MKO Abiola ne ya samu rinjayen kuri’u a lokacin zaben.

Idan zaku tuna abaya dai tsohun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Abiola da lambar girma ta GCFR.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatocin Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta a Asabar dinnan

Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa. Shugaba Trump ya sanar...

Rukunin farko na Alhazan jihar Kebbi guda 420 sun tashi zuwa Madinah

Rukunin farko na maniyyata 420 daga jihar Kebbi sun tashi daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello International Airport da ke Birnin Kebbi, zuwa...

Mafi Shahara