DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta sanya dalibai aiki mai tsauri a cikin makarantu

-

Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi gargadi ga malaman makarantu da kada su umurci dalibai yin ayyuka masu tsauri a ciki ko wajen makaranta.

Google search engine

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai.

Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wajen ba da ilimi ne da jagoranci, kyautata ɗabi’a ba wajen bautar da dalibai ba.

A wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai wata makarantar koyar da larabci da ke Kano, ya tarar da dalibai su na aiki mai wahala a cikin makarantar .

A bayyane gwamnan ya nuna rashin jin daɗi, tare da  tambayar shugaban makarantar game da sanya dalibai irin waɗannan ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

CDD ta horas da ‘yan jarida a Katsina kan yaki da labaran karya

Cibiyar bunkasa dimokradiyya ta CDD ta horas da ‘yan jarida a jihar Katsina kan aiki mai inganci. CDD ta ce wannan na a wani yunkuri na...

‘Yan bindiga sun halaka mutum 1,sun kuma mutane 5 a Zamfara

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya tare da sace mutane biyar,...

Mafi Shahara