DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana damuwarsa kan yadda malaman addini shiga harkokin siyasa, indaj ya bayyana cewa a yanzu malamai suna da tasirin gaske a kan masu zabe da harkokin siyasa

-

 

Sule Lamido

Google search engine

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, wanda ke nuna lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna sakamakon rasuwar babban dansa.

Tsohon ministan harkokin wajen ya koka da yadda malaman addini suke ci gaba da mamaye fagen siyasa, inda suke fitowa karara suna kamfen ga ‘yan takara tare da jagorantar mabiyansu kan wadanda za su marawa baya, ya kara da cewa duk da albarkar kasancewarsu shugabannin addini, malamai yanzu suna tallafawa masu neman mulki.

A cewar sa kamata ya yi malamai su tsaya a matsayinsu na malamai, ‘yan siyasa su tsaya a matsayinsu na ‘yan siyasa domin samun daidaito da adalci ga al’ummar da ake jagoranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara