Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami'in Binance cewa 'yan majalisa 3...

Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami’in Binance cewa ‘yan majalisa 3 sun nemi cin hancin $150m

Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami’in kamfanin Binance Tigran Gambaryan wanda ya shafe watanni takwas yana tsare a hannun hukumomin Nijeriya bisa zargin rashawa.
Gambaryan wanda dan kasar Amurka ne, an sake shi bayan da gwamnatin kasar ta shiga tsakani, sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya zargi gwamnatin Nijeriya da tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ‘yan majalisa uku sun nemi ya basu cin hanci na dala miliyan 150.
A martanin gwamnatin, ta hannun ministan yada labarai Mohammed Idris, ta ayyana kalaman a matsayin yunkurin yada labaran karya.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata