DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba mu tsawaita wa’adin hidimta wa kasar matashiyar da ta caccaki Shugaba Tinubu ba – NYSC

-

Hukumar NYSC ta karyata zargin tsawaita wa wata ‘yar bautar ƙasa daga Legas, Rita Uguamaye (Raye), aikin watanni biyu saboda sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Raye ta shahara a kafafen sada zumunta bayan ta wallafa bidiyo a TikTok tana koka da tsadar rayuwa da hauhawar farashi, tare da sukar Tinubu da kiran sa “shugaba mara tausayi.”

Google search engine

Daga baya, Raye ta ce ana yi mata barazana daga jami’an NYSC saboda bidiyon, inda ta ƙi goge shi tana mai cewa ta faɗi gaskiya ne.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa biyo bayan zargin da Raye ta yi, mutane da dama ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, sun yi Allah-wadai da barazanar da aka ce ana yi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan...

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan...

Mafi Shahara