DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyarsa ta Al Nassr har zuwa shekarar 2027

-

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya a hukumance, inda zai ci gaba da zama a birnin Riyardh na kasar har zuwa shekarar 2027.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, inda a hoton Ronaldo yake rike da riga mai lamba “2027” tare da shugaban kungiyar Al Nassr, Abdullah Almajid.

Google search engine

Sanarwar ta tabbatar da cewa Ronaldo, wanda kuma ke rike da mukamin kyaftin din kungiyar, zai ci gaba da aiki tare da Al Nassr na tsawon shekaru biyu.

Ronaldo ya kuma bayyana jin dadinsa a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara