DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yawan dogaro da kasashen waje ke hana Nijeriya samun ci gaba

-

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatocin Nijeriya da sauran kasashen Afirka kan yadda suke dogaro da tallafin kasashen waje, da rashin shugabanci nagari, da gazawar tsarin dimokradiyya.

Obasanjo ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na Afreximbank karo na 32 a Abuja a ranar Juma’a, inda ya ce kasashen Afirka sun kasa samun ci gaba da rashin inganci a tsarin mulki da kuma gudanar da mulki yadda ya dace.

Google search engine

A cewarsa, kasashe kamar Nijeriya, Masar, Habasha, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da Afirka ta Kudu, ya kamata su jagoranci ayyukan ci gaban nahiyar idan aka yi la’akari da yawan al’umma, albarkatunsu,da karfin tattalin arzikinsu.

Ya ce a maimakon haka, wadannan kasashe sun ci gaba da samun koma baya saboda rashin kyayyawan jagoranci.

Obasanjo ya bayyana cewa idan anason ci gaban Afrika sai dai idan wadannan manyan kasashen sun fara nuna ci gaba mai ma’ana da kyakkyawan jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara