DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bayan shafe watanni 23, Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

-

Ta dai tabbata, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC ta kasa.

Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya ajiye mukamin nasa da yammacin Juma’ar nan, kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito. Hakan na zuwa ne ‘yan kwanakin bayan takaddamar da ta biyo bayan babban taron jam’iyyar na shiyyar arewa maso Gabas a Gombe, inda nuna goyon bayan takarar shugaba Tinubu a jam’iyyar a azben 2027 ba tare da ayyana Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba da gandujen ya yi, ya janyo cece-kuce.

Google search engine

Rahotanni sun ce Dr. Ganduje ya gabatar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin saukarsa daga kujerar. To amma jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta lallashi Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya ajiye mukamin nasa domin bai wa jam’iyyar damar tsara dabarun tunkarar zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu wani jami’in gwamnatin jihar Plateau da ya zo yi mana ta’aziyyar mutanenmu da aka yi ajalinsu – Sarkin Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamalli, ya nuna damuwarsa kan yadda babu wata tawagar jami'an gwamnati daga Jihar Plateau da ta zo Zaria...

Za a yi wa Alhaji Aminu Dantata Sallar Jana’iza ta ‘Salatul Ga’ib’ a Kano

Shugaban majalisar Malamai ta kasa reshen jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya ce za su yi wa marigayi Aminu Alhassan Dantata, Salatul Ga’ib wato jana’izar...

Mafi Shahara