Yar’adua ya rubuta takardar damka min mulkin Nijeriya a lokacin, amma wani na kusa da shi ya rike ya ki gabatar da takardar gaban majalisar dokoki – Good Luck Jonathan
A karon farko bayan barinsa a ofis, tsohon shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana irin rikicin siyasar da ya biyo bayan rashin lafiyar tsohon Shugaban Kasa, marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua.
Jonathan ya bayyana cewa, a lokacin, shirye yake da ko mai zai faru a cikin Fadar Shugaban kasa da ya ajiye mukaminsa na Mataimakin Shugaban kasa.
Goodluck ya yi wannan bayanin ne a wata tattaunawa da Rainbow Book Club inda ya kara da cewa, Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua sanya ma takardar mika ragamar shugabancin Nijeriya gare shi amma wani makusancin marigayin wanda bai bayyana kowane ne ba ya hana ta isa majalisar.
Wannan lamari da ya jefa kasar cikin rudanin siyasa, sakamakon wanda zai cigaba da jan ragamar shugabancin kasar.
Idan ba a manta ba, a 2009, ‘Yar’adua ya fita kasar waje don neman lafiya ba tare da sanar da majalisa ba ko mika ragamar shugabanci ga Jonathan kamar yadda doka ta tanadar.