Jam’iyyar PDP na shirin gudanar da babban taronta a yau Litinin 30 ga Yuni, 2025 a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, yayin da rikici ya kara ta’azzara tsakanin bangarori biyu na shugabancin jam’iyyar.
Rahoton Jaridar Daily Trust ya ambato bangaren shugaban riko na kasa, Umar Damagum, da Sanata Samuel Anyanwu sun bayyana taron a matsayin “Taron Caucus”, tare da gayyatar masu ruwa da tsaki.
Sai dai, mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu, Amb. Taofeek Arapaja, tare da mambobi 11 na NWC, dake samun goyon bayan bangaren Gwamna Seyi Makinde na Oyo, wanda ya hada da gwamnonin Enugu, Bayelsa, Osun da Zamfara, da mambobin NWC 11 da wasu jiga-jigan jam’iyyar, sun dage cewa dole a gudanar da taron NEC kamar yadda aka tsara.
A daya bangaren kuma, tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda ke samun goyon bayan gwamnonin Plateau, Taraba, Adamawa, Bauchi da shugaban rikon kwarya Umar Damagum, na bukatar a dage taron kuma a maido da Anyanwu kan mukaminsa.