Sanatocin jam’iyyar PDP daga jihar Osun, Sanata Adenigba Fadahunsi daga Osun ta Gabas da Sanata Olubiyi Fadeyi mai wakiltar Osun ta Tsakiya, sun sake bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma kudirin sake neman wa’adin Mulki a 2027.
A Yayin da suke zantawa da manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, sanatocin sun yaba da irin ayyukan raya kasa da Tinubu ya kawo a mazabunsu da kuma irin jagorancin kwarai da ya nuna tun bayan hawansa Mulki.
Fadeyi, wanda ke shugabantar kwamitin muhalli a Majalisar Dattawa, ya ce mutanen Osun ta tsakiya za su marawa Tinubu baya da kuri’unsu a 2027.
Kazalika shima Sanata Fadahunsi cikin rahoton jaridar The Nation, ya yabawa Shugaban kasa bisa amincewarsa da ware kudade a kasafin kudin 2025 domin gyaran babban titin Ibadan zuwa Ilesa, wanda ke da matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci a jihar da kasa baki daya.



