Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin karin manyan mataimaka na musamman guda 19, domin ƙarfafa harkokin mulki da inganta ayyukan gwamnati.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir na da kusan mataimaka 290 kafin wadannan mukamai, waɗanda suka haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman da kuma Masu Ba da Rahoto na Musamman.
Gwamnatin jihar ta Kano ta bayyana ƙwarin guiwa cewa sabbin waɗanda aka naɗa za su yi amfani da ƙwarewarsu da jajircewarsu wajen taimakawa tafiyar da mulki bisa hangen nesa a jihar.



