Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Henry Seriake Dickson, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yakar matsalar sayen kuri’u da kuma murɗa sakamakon zaɓe, yana mai gargaɗi cewa irin waɗannan ayyuka na barazana ga ginuwar dimokuraɗiyya a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Seriake Dickson ya ce wajibi ne masu ruwa da tsaki su ɗauki nauyin taruwa domin fuskantar maguɗin zaɓe da kuma mummunar al’adar tsara sakamakon zaɓe tun kafin a kaɗa kuri’a.
Tsohon gwamnan Bayelsa ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ‘yan siyasa masu kudi da iko ke amfani da talauci da rashin ilimi wajen rinjayar masu kaɗa kuri’a ta hanyar raba kudi da kayan tallafi.



