Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Banshika a karamar hukumar Hong, jihar Adamawa.
A wasikar da aka sanya ranar 29 ga Yuni, 2025, Babachir ya ce ficewarsa ta fara aiki nan take, tare da bayyana cewa zai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga a nan gaba kadan.
Ya ce matakin na daya daga cikin shirinsa na hada kai da sauran ‘yan Najeriya domin gyara kasar daga kuskure da gazawar tsohuwar jam’iyyarsa ta APC kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ambato.