![]() |
NAHCON |
Yayin da wa’adin hukumar alhazan Nijeriya NAHCON na kammala biyan kudin aikin hajji ke cika a yau 31 ga watan Janairu, rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar kara wa’adin kasancewar zuwa yanzu alhazai dubu 51,447 ne kacal suka kammala biyan kudinsu, duk da cewa Nijeriya ta samu gurbin mutum 95,000.
Sai dai wasu jami’an hukumar sun danganta rashin biyan kudin da tsadar kudin aikin hajji da kuma karancin lokacin biyan kudin da aka sanya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Farashin kudin aikin hajjin bana ya kai naira milyan N8.3m zuwa milyan N8.7m a sassan Nijeriya.