Gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Alhamis cewa tana shirin sauya dokar zaɓe domin ba wa matasa masu shekaru 16 da 17 damar kada kuri’a a zaɓukan gama gari.
Matakin na zuwa ne bayan jam’iyyar Labour mai mulki ta sha alwashin aiwatar da sauyin tun kafin ta karɓi mulki a bara, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Haka kuma, yana ɗaya daga cikin jerin sauye-sauyen tsarin dimokuraɗiyya da gwamnati ke shirin aiwatarwa, musamman ganin yadda ƙasa ke fuskantar koma baya a sha’anin fitowar jama’a wajen yin zaɓe.
Sai dai ana sa ran matakin zai haifar da ce-ce-ku-ce, kasancewar masu adawa da sauyin sun taɓa zargin cewa yana da wata manufa ta siyasa, domin ana ganin matasa sun fi karkata ga jam’iyyar Labour mai ra’ayin hagu.