Home Sabon Labari Taskar Guibi: 03.06.2020

Taskar Guibi: 03.06.2020

114
1

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha daya ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Biyo bayan sanarwar shugaban kasa ya amince kulle ya koma daga karfe goma na dare zuwa karfe hudu na asubah, da bude wuraren Sallah da ibada, da sauransu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, da kuma sakar wa kowacce jiha marar sai ta ga dama ta yi aiki da amincewar tasa, kowacce jiha na yi yadda ta ga ya fi mata daidai. Misali a jihar Kaduna babu wannan walwalar ta sallah a masallaci ko zuwa coci-coci da sauran walwalar da shugaban kasa ya sanar, har sai an gama tattaunawa da tsattsarawa da shugabannin al’umomin da abin zai shafa kafin a dauki matakin sassautawa. Shi kuwa gwamnan Katsina ya amince zai bi amincewar ta shugaban kasa. Ganduje na Kano kuwa ya ce za a dore da yadda ake a yanzun a jihar sai nan gaba kadan. Gwamnatin jihar Legas ma ta ce tunda can ne shalkwatar kwaronabairos, ba batun aiki da amincewar shugaban kasa, za a ci gaba da kulle. Sai dai wasu na korafin kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tufka da warwara. Ya ba da umarni, ya kuma ce sai gwamnan da ya ga dama ya bi umarnin nasa. Wasu kuma na korafin gwamnonin ne suka mayar da shi kamar ba shugaban kasa ba, ya ce ga yadda za a yi, gwamnonin su ce ga yadda suka ga dama su yi. Suka ce misali akwai umarni daga gwamnatin tarayya na ma’aikata daga matakin albashi na goma sha hudu zuwa sama su hanzarta komawa aiki, suna zuwa karfe takwas suna tashi karfe biyu. Su kuma gwamnonin da ba su dage kullen ba sun ce kada kowa ya fita. Ya za a yi kenan? Ma’aikaci na fita kotun tafi-da-gidanka za ta damke shi ta masa tara ke nan.

2. Jiya kamar su ministan labaru Lai Mohammed sun ga hannunka mai sanda da na yi ga Arewawa a kan wata’yar makaranta da aka yi wa fyade a wani coci da ke jihar Edo, aka kuma kasheta, har fadar shugaban kasa, da fadar shugaban ‘yan sabdan Nijeriya, da fadar gwamnan jihar Edo, da fadar gwamnatin daliban Nijeriya, da fadar kungiyoyin matan Nijeriya, da sauran fadoji suka dauki dumi a kai, da umarni daban-daban, na kuma kawo labarin wata ‘yar shekara goma sha biyu da ke mu’amalarta da maza har kusan su goma sha biyar a lokuta daban-daban suna ba ta na kashewa, da tunda yarinya ce shekarunta ba su kai ba, ya zana fyade, a yanzun gwamnatin tarayya ta bakin Lai Mohammed ta ba da umarnin a binciki lamuran guda biyu don daukar mataki. Sai dai wasu na korafin cikin tsakanin karshen makon da ya gabata zuwa jiya an kashe wasu manya a Arewa kamar Hakimin ‘Yan Tumaki Maidabino da ke jihar Katsina, da sauransu, ba a ji Femi Adeshina ko Garba Shehu sun fitar da kaduwar gwamnati a kai ba.

3. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Akinwumi Adeshina, ya kuma ba shi tabbacin goyon bayan sake darewar kujerar shugabancin Bankin Raya Afirka AfDB, duk da zargin da wasu ke masa mara tushe na rashawa. Haka ita ma majalisar wakilai ta ba shi tabbacin goyon bayan sake yin wata shekara biyar a kujerar.

4. Majalisar Dattawa ta amince wa shugaban kasa ya ciwo bashin da ya nemi izinin zai ciwo na dala biliyan biyar da rabi. Ita ma majalisar wakilai ta ce ya ciwo ba matsala.

5. Gwamnatin Tarayya ta ce a walwalar zuwa sallah da coci da ta amince a yi, ta ce kada ibada ta wuce tsawon awa guda, Sallah kuma kada ta wuce minti goma, da jan hankalin limamai da ke jan dogayen sura a Sallah, su dinga jan gajajjeru. Sannan an nemi masu yawan shekaru ko lalura su dan tsahirta da zuwa jam’i, a kuma dinga zuwa masallaci da silifas saboda in an idar dandana kowa ya dau silifas dinsa ya yi gaba ba turmutsitsi, kuma kowa ya je da sallayarsa.

6. Gwamnatin tarayya na shirin horas da matasa manoma su dubu dari bakwai da saba’in da hudu noma daban-daban.

7. Wasu sun kashe a kalla mutum uku a wani hari da suka kai jihar Binuwai.

8. Yau da gobe, kamar jiya, akwai walwalar fita don nemo abincin ci gaba da kulle a jihar Kaduna. Na zaga jiya, na lura akwai cunkoson ababen hawa, ga tsadar mota ko babur ko Nafef, kodayake masu acaba da nafef, sun ce ‘yan sanda ne ke matsa musu da kamu da kuma cinsu tara ba ‘yar kadan ba. Wannan ya sa inda za ka hau hamsin, sai ka biya naira dari biyu. Haka nan na lura ‘yan bas musamman masu yin Sabon Tasha, na cunkusa fasinja ba sa kiyayewa da tazarar da aka ce wajen zama a cikin mota. Kuma kashi biyar ne kawai, cikin dari na jama’ar da na gani na karakaina jiya suka sanya takunkumi.

9. Fitaccen makadin nan na rege Majek Fashek ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara hamsin da bakwai a duniya.

10. A jihar Adamawa ana zargin wani dan sanda ya bindige wani da ya hana shi naira dari ya mutu.

11. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a yanzun akwai magunguna barkatai a duniya da ske ta kokarin gwada su wajen maganin kwaronabaros.

12. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi shiru. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

13. Daliban jami’ar jihar Kaduna na nan sun ci gaba da karatu a gida, malamansu na koyar da su ta hanyar intanet.

14. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwarona su 241 a jihohi kamar haka:

Legas 142
Oyo 15
Abuja 13
Edo 11
Delta 10
Kaduna 9
Ribas 9
Barno 8
Jigawa 4
Gwambe 3
Filato 3
Oshun 1
Bauci 1

Da ke nuna kowacce jiha a yanzun tana da:

Legas 5277
Kano 970
Abuja 687
Katsina 371
Edo 336
Oyo 317
Kaduna 297
Barno 296
Ogun 280
Jigawa 274
Ribas 248
Bauci 241
Gwambe 164
Sakkwato 116
Kwara 111
Filato 108
Delta 98
Nasarawa 80
Zamfara 76
Yobe 52
Oshun 46
Akwa Ibom 45
Adamawa 42
Ebonyi 40
Imo 39
Kabbi 33
Neja 33
Ondo 28
Bayelsa 21
Ekiti 20
Inugu 18
Taraba 18
Abiya 15
Anambra 11
Binuwai 9
Kogi 2 amma Gwamna Yahya ya ce 1
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 10,819
Jimillar wadanda suka warke 3,239
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 314
Jimillar wadanda ke jinya 7,266

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga ma’abucin soshiyal midiya, har ma da jaridun jiya, zai ga labarin yadda shugaban hukumar kwastam na kasa bakidaya Hamid Ali ya yi koli-koli da wani da suke nema na aure da wata ya tandara shi da kasa, ya aureta. Aka ruwaito cewa wanda ya ji zafin kayen, ya garzaya gaban kuliya yana neman sai ta biya shi miliyoyin da ya kashe mata a lokacin da suke samartaka. To jiya ya fito ya ce kafofin da suka fallasa cewar da ya yi sai ta biya shi hidimar da ya mata, sun yi ba da izininsa ba. Shi a yanzun ya hakura ya rungumi kaddara yana mata fatan alheri, duk hidimar miliyoyin da ya mata ya yafe. Sai dai wasu na cewa hmm! Ruwa ba ya tsami banza, ko in ka ji gangami da labari.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here