Kungiyoyin farar hula da jam’iyyun adawa a jihar Kebbi sun nuna rashin jin daɗinsu kan matakin da ‘yan majalisar dokokin jihar na ba da gudummawar motoci guda 25 ga ƙungiyar siyasa mai suna Tinubu/Kaura 2 Terms (TKT), wadda ke fafutukar ganin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris sun samu wa’adin mulki na biyu a 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa motocin da aka bayar kowacce daga cikinsu na tsakanin naira miliyan 3.5 zuwa miliyan 6, bisa farashin motoci a shafin Cars45.com.
Shugaban majalisar dokokin Kebbi, Alhaji Muhammad Usman-Zuru, ne ya miƙa motocin ga ƙungiyar a madadin sauran mambobin majalisar guda 25, yana mai cewa hakan na cikin alkawarin da suka dauka lokacin da aka ƙaddamar da ƙungiyar a ranar 20 ga Mayu, 2025.
Sai dai wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ‘yan adawa da masu fafutuka, inda suka zargi majalisar da cin amanar jama’a da amfani da dukiyar gwamnati don biyan bukatun siyasa.
Masu suka sun bayyana cewa bai kamata ‘yan majalisar da ke matsayin wakilan jama’a ta maida kanta ‘yan kamfen ba, musamman a lokacin da ake fuskantar matsaloli na tattalin arziki da bukatar kashe kudi a bangarori masu mahimmanci kamar lafiya, ilimi da ababen more rayuwa.


