Tallafin da gwamnatin Nijeriya ke biya a kan wutar lantarki ya tashi daga Naira biliyan 610 a 2023 zuwa Naira tiriliyan 1.94 a shekarar 2024, duk da karon farashin Band A da aka yi a watan Afrilu 2024, kamar yadda jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Wannan karin yana nufin an samu karuwar kashi 219.67 cikin 100 na kudaden da gwamnati ke kashewa don rage nauyin farashin wuta ga ‘yan ƙasa.
Hukumar kula da bangaren lantarki NERC da wasu masana tattalin arziki sun bayyana cewa karin ya faru ne bayan sakin darajar Naira da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar a watan Yuni 2024, da kuma cire tallafin man fetur, wanda hakan ya haifar da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
A cewar NERC, gwamnati ta kashe jimillar Naira tiriliyan 1.94 domin cike gibin da ke tsakanin farashin hakikanin wuta da kudin da ake karɓa daga wajen jama’a.
Sai dai duk da wannan adadi mai yawa, rahoton ya nuna cewa gwamnati ta biya kawai Naira miliyan 371.34 daga cikin wannan nauyin, wanda hakan ke wakiltar ƙasa da kashi 0.02 cikin 100 na adadin da ake binsu.
Tallafin wutar lantarki da gwamnatin Nijeriya ke biya ya haura Naira tiriliyan 1.9 a 2024 – Rahoton Punch
-


