DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yadda ‘yan cabals ke turawa Buhari takardu a boye don ya sanya musu hannu – Tsohon shugaban ma’aikata, Gambari

-

Tsohon shugaban ma’aikata na Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana yadda wasu makusantan shugaban suka rika tsallake shi tare da mika takardu kai tsaye domin ya sanya musu hannu.

Farfesa Gambari ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Inside Sources na Channels Television a ranar Juma’a.

Google search engine

A cewarsa, duk da cewa Shugaba Buhari ya bayyana cewa dole ne duk wasu takardu su rika bi ta hannun shugaban ma’aikata, wasu daga cikin mukarrabansa suna amfani da saukin zuciyarsa da sanin lokutan rauninsa, suna mika bukatunsu kai tsaye.

Farfesa Gambari, wanda ya rike mukamin daga Mayu 2020 zuwa Mayu 2023 bayan rasuwar Abba Kyari, ya ce ko mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta hanyarsa yake tura takardunsa amma ‘yan cabal sai dai su tsallake sa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara