Shugaban kwamitin kudi da gyaran haraji na Shugaba Tinubu, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya yanzu tana kashe ƙasa da kashi 50 cikin 100 na dukkanin kudaden shigarta wajen biyan basussuka.
A yayin wata hira a taron PwC Executive Summit da aka gudanar a Legas, Oyedele ya ce kafin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, Nijeriya tana kashe kusan kashi 97 cikin 100 na dukiyar da take samu wajen biyan basussuka.
A cewarsa, gwamnatin ta riga ta biya wasu tsofaffin basussukan ƙasashen waje da suka kai fiye da dala biliyan 7, asusun ajiyar kuɗin cikin gida ya karu daga dala biliyan 4 zuwa biliyan 20.
Har ila yau, harajin da ake karɓa daga mutane da kamfanoni ya tashi daga ƙasa da kashi 10 zuwa 13.5 cikin 100 a cikin shekaru biyu kacal.



