Majalisar wakilan Nijeriya ta fara nazarin kudirin doka da zai haramta wa ma’aikatan gwamnati da iyalansu amfani da makarantu da asibitocin kudi.
Rahoton Jaridar Daily Trust ya ce Hon. Amobi Ogah ne ya gabatar da kudirin, inda ya ce manufar ita ce tilastawa jami’an gwamnati su rika amfani da cibiyoyin gwamnati domin farfado da martabarsu.
Ya zargi yadda gwamnati ke gudun amfani da kayan gwamnati wanda ke haifar da durkushewar ilimi da lafiya, tare da cewa dokar za ta rage cin hanci da karfafa tsarin gwamnati.



