Wani lauya, Ekemini Udim, ya bayyana cewa kotu ba ta bayar da umarnin a mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan zauren majalisar dattawa ba, bayan dakatarwar watanni shida da aka yi mata a watan Maris.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Udim ya ce: “Mai shari’a bai ce a mayar da sanata Natasha ba. Abin da ya ce shi ne Majalisar Dattawa ta sake nazari kan dokokinta.”
Sanata Natasha, da aka dakatar bisa zargin saba dokokin majalisa da kuma furucin cin zarafi da ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ta nemi komawa kujerarta ranar Talata, amma jami’an tsaro suka hana ta shiga harabar majalisa.
Bayan haka, ta bayyana rashin jin dadinta kan lamarin tare da cewa za ta tuntubi lauyoyinta domin daukar mataki na gaba.



