Sanata Yusuf Datti Baba Ahmed da ya yiwa Peter Obi takarar mataimaki a zaben 2023 karkashin jam’iyyar Labour Party yace, Obi nada damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar koda kuwa ba shine zai masa mataimaki ba a zaben 2027 da ke tafe.
Baba Ahmed yayi kalaman nasa ne a yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace Mutane biyu ne yake da matukar girmamawa a gare su kuma daya daga cikin su shi ne Peter Obi
Yakara da cewa hulda da gamayyar jam’iyyu da Peter Obi ke yi a karkashin inuwar ADC ba cin amanar jam’iyya ba ne, illa dai wani sabon yanayi da siyasar Nijeriya ta shiga.



