Gwamnatin Jihar Yobe ta musanta rahotannin da ke cewa Gwamna Mai Mala Buni na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Daraktan Yada Labarai da Harkokin Jama’a na Gwamnan, Mamman Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.
Mohammed ya ce an riga an musanta wannan rahoto tun da farko, don haka bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba.
A cewarsa, batun cewa Buni zai koma jam’iyyar ADC ba gaskiya ba ne, rahoton kuma bai da tushe balle makama.