Kasa da wata daya kafin fara tsarin rarraba man fetur kai tsaye daga matatar Dangote, masu jigilar fetur a Nijeriya sun bukaci kamfanin da ya janye wannan kudiri nasa.
Daga ranar 15 ga Agusta, kamfanin Dangote zai fara samar da man fetur kai tsaye zuwa gidajen mai, kamfanonin sadarwa, bangaren sufurin jiragen sama, da sauran manyan wurare masu amfani da man fetur.
Sai dai, masu jigilar man fetur karkashin kungiyarsu ta Natural Oil and Gas Suppliers Association of Nigeria sun bayyana damuwa cewa wannan mataki na iya haddasa asarar ayyukan yi da dama a bangaren.
A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Shugaban kungiyar NOGASA, Benneth Korie, ya ce shirin Dangote na kauce wa tsarin rarraba man da aka saba da shi zai kawo tangarda ga harkar samar da man fetur da iskar gas a Nijeriya, kuma zai jefa rayuwar dubban ma’aikata cikin hadari.